Har yanzu akwai ƙasashen Afrika 34 na ƙarkashin dokar kulle sakamakon cutar korona

0
2780

Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Talata cewa, kasashen Afrika 34 suna karkashin cikakkiyar dokar kulle sakamakon fargabar da ake da shi game da yaduwar annobar COVID-19 a nahiyar Afrika.

Kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana cikin sabbin bayananta game da halin da ake ciki dangane da yaduwar annobar COVID-19, ta ce ya zuwa ranar Talata, kimanin kasashen Afrika 34 suna karkashin cikakkiyar dokar kulle, yayin da kasashe 11 sun fara takaita shigi da fici zuwa kasashensu saboda yaduwar cutar.

Cibiyar ta ce an sabunta dokar hana fita da dare a kasashen Afrika 34 a matsayin matakan da za su takaita bazuwar cutar.

Sai dai kuma CDC Afrika ta bayyana cewa, wasu kasashen nahiyar 31 sun fara sassauta matakan, inda suka ba da damar yin zirga zirga a wajen kasashensu, da ba da damar kara bude harkokin kasuwanci, da kuma baiwa mabiya addinai damar bude wuraren ibadu, amma su takaita taruwar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here