Hauhawar Masu Korona A Legas Ya Sanya Muka Dakatar Da Bude Wuraren Ibada

0
146

Gwamnatin jihar Legas da ke kudu ta ce ta dage lokacin da za a bude majami’u da masallatai har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Gwamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu ya ce an yanke hukuncin hakan ne sakamakon yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar korona a jihar.

A baya dai gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar bude masallatai da majami’u a ranakun 19 da 21 na wanann wata.

Bbc Hausa sun labarto cewa; a wani taron manema labarai da gwamnan ya yi ya nuna matakin dakatar da budewar wuraren ibadun nan take na da nasaba da yadda ake kara samun karuwar wadanda ke harbuwa da cutar coronavirus a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here