32.5 C
Nigeria
Thursday, December 9, 2021

Hukuncin Kisa Ya Kamata A Rinƙa Yankewa Wanda Suka Aikata Laifin Fyade “. Hajiya Asiya Balaraba Ganduje 

Must read

-“Fyaɗe Babban Laifi Ne Da Bai Kamata A Sassautawa Duk Wanda Ya Aikata Ba, Kuma Ma Addinin Musulunci Ya Yi Kira Ga Masu Imani Da Su Riƙa Runtsewa Idanuwansu Ka Da Su Yi Wa Matan Da Ba Nasu Ba Kallon Ƙurullah Balle Su Ji Sha’awarsu Har Ta Kai Su Ga Neman Sai Sun Biya Buƙatarsu Ta Kowane Hali”. Cewar Balaraba Ganduje.

Duba da yadda matsalar fyaɗe ta ke cigaba da zama ruwan dare mai gama duniya a Nageriya, Ni Bashir Abdullahi El-Bash, na samu damar tattaunawa da uwar marayu, garkuwar matasan Arewa, ƴar mai girma gwamnan Jihar Kano, tauraruwar matan Arewa, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, (Fulanin Zannan Laisu Fika) dangane da wannan matsala ta cin zarafin ƴaƴa mata da yara maza ta hayar yi musu fyaɗe da kuma yadda ta ke kallon lamarin a mahanga irin ta addinin Musulunci.

A ya yin tattaunawar tamu, Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta ba da shawarwari masu matuƙar muhimmanci ga ɓangaren masu doka da ɓangaren iyaye da ƴan mata da kuma al’umma gabaki ɗaya. Tunda farko na fara ne da yi mata tambaya kan yadda ta ke ji a daidai wannan lokaci da rahotannin yi wa mata fyaɗe ya ke cigaba da yawaita a Nageriya ? ga amsar da ta bayar :

“El-bash da farko sai dai mu ce Innalillahi Wa’inna’ilaihirraji’un, domin wannan matsala ta fyaɗe babbar musifa ce kuma annoba ce ba ƙarama ba. A matsayina na uwa na kaɗu matuƙa da na ke samun labarai da rahotannin yadda ake cin zarafin ƴaƴa mata ta hanyar yi musu fyaɗe, na yi tir da Allah wadai da masu aikata wannan ɗanyen aikin. Wannan matsala ta girgiza ni matuƙa, kuma a kullum da ita na ke kwana da ita na ke tashi ina takaicin lamarin da kuma nazarin hanyoyin da ya kamata abi domin a magance matsalar”.

Ranki daɗe kin ce ki na nazarin hanyoyin da ya kamata abi domin a magance matsalar, kafin hakan shin ko kin yi tunanin abubuwa da su ke haddasa wannan matsala kuma ta ke cigaba da girma a kullum ? Ni El-bash na tambaye ta.

“Eh to ni dai a tunanina wannan ɗabi’a ta fyaɗe da wasu su ke aikatawa dabbanci ne kawai da rashin hankali, domin idan mu ka kallin yadda matsalar ta ke za mu ga cewar ba wai iya ƴan mata baligai ake yi wa fyaɗen ba har ma da yara ƙanana maza da mata ƴan ƙasa da shekaru 5, kaga kenan in ka kalli matsalar za ka ga cewa ba ta da alaƙa da neman biyawa kai sha’awar jima’i sai dai a ce rashin hankali da dabbanci irin na wasu ƴan adam ɗin”. Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta bayyana. Daga nan sai ta ƙara da cewa:

“Amma duk da haka ina tunanin wannan matsala ta na da alaƙa da rashin Imani, saboda sai ka iske an kama tsoho ɗan shekaru sama da 50 ya yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe, saboda dabbanci irin nasa. Sannan a wasu lokutan ina tunanin cewa wasu ƴan matan su kan fuskanci fyaɗe saboda saɓawa addinin musulunci wajen sanya tufafi da fitar da tsiraici. A tunanina waɗannan abubuwa su na daga cikin abunuwan da ke haddasa wannan matsala ta fyaɗe a Nageriya”. Cewar Hajiya Asiya Balaraba Ganduje.

A daidai wannan gabar Ni Bashir Abdullahi El-bash na ƙara da yi mata tambaya cewa: ranki daɗe kin bayyana yadda wannan matsala ta fyaɗe ta ke tayar miki da hankali da kuma abubuwan da ki ke tunanin su ne su ke haddasa faruwarta, shin waɗanne hanyoyi ya kamata abi domin ganin an magance matsalar gabaki ɗaya ?

Ga amsar da ta bayar: “El-bash akwai hanyoyi kamar guda 5 da ya kamata abi domin a magance wannan matsala. Daga cikin waɗannan hayoyi akwai rawar da gwamnati ce za ta taka, akwai kuma rawar da iyaye ne za su taka, akwai rawar da ƴan mata ne za su taka sannan kuma akwai rawar da al’umma ne gabaki ɗaya za su taka. Da farko dai gwamnati ta kafa doka a matakin tarayya da Jihohi duk wanda aka kama da laifin aikata fyaɗe to a yanke masa hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai. Su kuma alƙalai su tabbatar sun gudanar da aikinsu ba sani ba sabo duk wanda aka tabbatar ya aikata a hukunta shi ba tare da ɓata lokaci ba”. Inji Hajiya Asiya Balaraba Ganduje. Sannan kuma ta cigaba da cewa :

“Abu na biyu iyaye su tabbatar su na sa ido akan ƴaƴansu ƴan mata da ƴara ƙanana. Duk budurwar da za ta fita cikin shigar da ba ta dace ba to a sa ta dole ta sake shiga domin shigar banza ita ce ta ke surantawa ɓatagarin maza kyawun halittar ƴa mace har su ji su na sha’awar saduwa da ita ko ta halin ƙaƙa. Sannan a riƙa killace yara daga fita ƙofar gida idan har babu tufafi da hijabi ko ishashen mayafi a jikinsu. Ka da iyaye su riƙa aiken yara mata wuraren da ƙafa ta ke ɗaukewa ko a bar su na fita idan dare ya yi”. Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta faɗa. Daga nan ta ɗora da cewa:

“Daɗi da ƙari iyaye su tabbatar su na ba wa ƴaƴansu kulawa da biya musu buƙatunsu irin na rayuwar ɗan adam, domin rahotanni sun tabbatar da cewa wasu masu fyaɗen su kan yaudari yarinya da kuɗi su ja ta inda ba kowa su yi mata fyaɗe. Haka zalika iyaye su dena ɗorawa ƴaƴa mata ƴan mata da ƙanana talla domin talla ma hanya ce da ɓatagari su ke amfani da ita wajen nunawa yarinya cewa ta kai musu abin da ta ke siyarwa wani waje da ba kowa daga nan su yaudare ta su yi mata fyaɗe”. Inji Hajiya Asiya Balaraba Ganduje. Sai kuma ta cigaba ta na cewa :

“Wannan rigakafi kenan na kare afkuwar matsalar, sannan ya na daga cikin rawar da iyaye za su taka bayan faruwar matsalar Allah ya kiyaye, idan matsalar ta faru ka da su ɓoye su yi gaggawar sanar da hukuma har sai an kamo wanda ya aikata laifin an hukunta shi. Abu na uku, ƴan mata su riƙa sanya tufafi irin wanda shari’ar musulunci ta ce kafin su fita waje. Allah ya yi hani da tabarruji ya gargaɗi mata musulmai da ka da su yi tabarruji irin na al’ummar jahiliyya, ma’ana ka da su yi ado su fita su na masu bayyana tsiraici ka da su bayyana adonsu sai ga mazajensu da muharramansu. Saboda haka mata su kame kawunansu daga yin duk wata shiga wacce za ta tada sha’awar mazajen da ba nasu ba”. Cewar Hajiya Asiya Balaraba Ganduje. Sannan ta cigaba da cewa :

“Abu na huɗu jama’a su ba da gudunmawa wajen yaƙi da wannan masifa ta fyaɗe duk wanda ake zargin ya aikata fyaɗe idan har akwai wanda ya ke da hujja to ya yi gaggawar zuwa gaban hukuma ya ba da shaida domin a hukunta wanda ya aikata. Sannan kuma jama’a su guji aibata duk wacce aka yi wa fyaɗe, domin ita ma ba da son ranta aka yi mata ba, bala’i ne ya faɗa mata, babu wanda ya fi ƙarfin Allah ya jarabce shi”. Inji Hajiya Asiya Balaraba Ganduje. Sai kuma ta ƙarƙare da cewa :

“Idan ya kasance jama’a su na ƙyamar matan da aka yi wa fyaɗe to su na ƙara jefa su ne a cikin halaka domin su na jin damuwar an yi musu faɗe da kuma takaicin jama’a su na tsangwamarsu, wacce ba ta da ƙarfin tawakkali za ta iya kashe kanta, in kuma ƙaramar yarinya ce za a iya jefa rayuwar iyayenta cikin ruɗani da neman barin gari ko unguwa. Saboda haka ina kira ga jama’a su dena ƙyamar waɗanda aka yi wa fyaɗe, a madadin ƙyama su nuna musu ƙauna, su na ba su haƙuri su na rarrashinsu har Allah ya ba su kwanciyar hankali. Dag ƙarshe, kamar yadda na faɗa tunda farko, ina fatan hukumomi za su yi dokokin da za a riƙa yankewa duk wanda ya aikata fyaɗe hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai a gidan yari domin hakan shi ne hanyar kawo ƙarshen matsalar”.
Inji – Hajiya Asiya Balaraba Ganduje.

- Advertisement -spot_img

More articles

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest article