ICPC Za Ta Binciki Ayyukan Da Aka Bada A Yi A Jihohi 16

0
194

Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka, ICPC ta ce tana bibiyar ayyuka 250 da aka bayar a gudanar a yankunna daban-daban a jihar Kwara.

Hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Rasheedat Okoduwa, inda ta ce wannan atisayen bibiyar ayyukan yana cikin mataki na biyu da zai gudana a jihohi 16 na fadin kasarnan.

Har wala yau hukumar ta ce; ayyukan an bayar da su ne a tsakanin 2015 da 2019 wanda kudinsu ya kai naira biliyan 4.1 tsakanin yankunan uku da ake da su wanda suke samun wakilcin Sanataci uku a jihar.

Sauran jihohin da ICPC din za su bibiyu ayyukan sun hada da  Kuros Ribas, Taraba, Ekiti, Ogun, Gwambe, Nasarawa, Kebbi, Kwara, Jigawa, Abia, Delta, Ebonyi, Neja, Ribas, Oyo da Kaduna.

Sun ce za su maida hankali wajen duba ayyukan da aka bayar a yi a sashen lafiya, ilimi, ruwan sha, noma, wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here