Ina jin ƙarfi a jikina fiye da yadda na ke ji shekaru 20 da suka gabata – Donald Trump

0
421

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa sam babu abin fargaba game da komawarsa White House gabanin sallamarsa daga Asibiti inda ya ce yanzu haka yana jin kwarin jiki fiye da yadda ya ke ji shekaru 20 da suka gabata.

Bayan ficewarsa daga Asibiti a safiyar jiya litinin don ganawa da magoya bayansa da suka yi dafifi a harabar wajen asibitin da nufin yi masa fatan alkhairi wanda ya haddasa masa kakkausar suka daga bangarori daban-daban ciki har da na lafiya Donald Trump ya ce baya shakkar wani batu na daban ya biyo baya domin kuwa ya samu cikakkiyar lafiyar iya komawa bakin aiki.

Trump wanda ya shafe kwanaki 3 kwance a asibiti, bayan isarsa fadar White House rahotanni sun ce ya cire mayanin rufe hancin da ke fuskarsa yayinda ya rika hada-hada da jama’a duk da kasancewar gwaji ya tabbatar da yadda kaso mai yawa na mutanen da ya ke tare da su sun kamu da coronavirus.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin jiya Litinin Trump ya ce ko kadan kada jama’a su razana da Covid, kar su bari fargabar cutar ta tauye rayuwarsu.

Zuwa yanzu dai Amurka miliyan 7 da dubu dari 4 ke dauke da cutar ta Covid-19 ciki har da dubu 210 da cutar ta kashe.

Sakon na Trump ya ci gaba da cewa tabbas zai bar asibitin tun a jiyan domin kuwa yana da kwarin jikin ci gaba da aiki yadda ake bukata.

Rfi Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here