Injiniya Mu’az Magaji ya sake dawowa ƙunshin gwamnatin Ganduje

0
494

Gwamnatin jihar Kano ta sake baiwa tsohon kwamishinan ayyuka Injiniya Mu’az Magaji sabon mukami a ƙunshin gwamnatin Ganduje.

Tun da farko Injiniya Mu’az Magaji ne ya bayyana sanarwar ba shi muƙamin a shafinsa na fasebuk, in da ya bayyana godiyarsa ga gwamnan bisa sake bashi damar yin aiki a gwamnatinsa a karo na biyu.

“Alhamdulillah, na sake samun dama a gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin yin aiki a matsayin Shugaban kwamitin Masana’antu na jihar Kano.”

Haka kuma Injiniya Mu’az Magaji shi ne shugaban shirin da Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya ke yi na shimfiɗa bututun Iskar Gas da zai taso daga jihar Kogi, ya ratsa ta birnin tarayya Abuja ya biyo ta jihar Niger zuwa Kaduna daga nan kuma ya kuma tsaya a jihar Kano.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watqn Aprilu ne gwamna Abdullahi Umar Ganguje ya tube Injiniya Mu’azu Magaji daga muƙamin kwamishina bayan wasu kalamai da suka nuna yana murnar rasuwar Abba Kyari.

A sakon da kwamishinan ya wallafa a Facebook, Injiniya Muazu, ya bayyana cewa “nasara, nasara. Najeriya ta tsira, Abba Kyari ya mutu a cikin annoba.”

Har kawo haɗa wannan rahoto babu wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar Kano dangane da sabon mukamin da tsohon kwamishinan ya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here