Jami’an ƴan sanda sun damƙe wani likita bisa zargin ƙone motoci 25

0
3268

Jami’an ‘yan sanda sun kwace wani faifan bidiyo da ke nuna likitan, Dr Ameet Gaikwad, wanda a ciki ana iya ganin likitan sanye da hular kwano yana shiga wasu gidaje daban-daban.

Ba a tabbatar da dalilain da ya sa wannan likitan aikata wanna laifin ba, amm ana ganin yana da tabin hankali.

Daga cikin motocin da ya kona, 13 na wasu likitoci ne da basu da wata alaka da Likita Gaikwad.

Likitocin na aiki ne a wata gunduma ta dabam, nesa da inda Dr Gaikwad yake aiki.

Shi dai likitan da ake tuhuma da wannan laifin babban likitan jiki ne inji ‘yan sanda, kuma sun ce babu wani rahoto na gaba tsakanin sa da sauran abokan aikinsa.

“Dangane da aikinsa, yawancin mutane sun ce mutumin kirki ne, kuma kwararren malami”, inji wani jami’in ‘yan sanda. “Kusan kowa a wurin aikinsa ya yi mamakin wannan labarin”.

Wani mai gadi ne ya kama likitan ma shekara 37 da haihuwa, kuma bayan an mika shi ga hannun ‘yan sanda, sun ce ya riga ya kona wasu motcin guda 10 a wannan yinin.

Sun je akwai tabbacin cewa shi ne ya kona wasu motocin guda 15 a wurare daban-daban a cikin wasu gundumomi biyu na jihar.

A halin yanzu dai liktan na tsare a hannun hukuma, kuma an shigar da kara akan laifukan da ake tuhumarsa da a ikatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here