Jami’an ƴan sanda sun damƙe wata Akuya bisa zargin aikata laifi

0
5609

Rahotanni daga kasar Indiya sun bayyana yadda wani jami’in dansandan kasar ya kama wata akuya da mai ita bisa aikata laifin barna da akuyar ta yi a wani lambun babban ma’aikacin gwamnati.

Ƴan sandan jihar Chhattigash suka dauki mataki akan mutumin da akuyar sa a sakamakon kama ta da aka yi tana cin ganye a lambun gundumar majistare da ke yankin.

Koda ya ke rahotanni sun bayyana cewar an bada belin mutumin da akuyar sa, amma ana tuhumar su da laifin karya doka da bannata kaya, a cewar daya daga cikin jami’an mai suna Ram Sewak Paikra daga Janakpur a gundumar Korea.

Jami’in ya kara da cewa “da farko akuyar da mai ita na hannun jami’an ‘yan sanda amma yanzu an bada belin su kamar yadda kundin tsarin mulki kasar sashe na 427 da 447 ya tanadar. kodashike akuyar ta dade tana aikata wannan laifi a cikin garin Janakpur dake da kwatankwacin kilomita 340 arewa daga birnin Raipur”.

An bada belin Abdul Hasan da akuyar tasa ne bayan ya furta cewar bazai sake barin akuyar ta aikata irin wannan mummunan laifi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here