Jami’an tsaro sun cafke masu buga kuɗin jabu

0
4282

Hukumar tsaron farin kaya a Sudan ko GIS a takaice, ta sanar da cafke wani gungu na masu buga kudin jabu. Hukumar ta ce an cafke manyan mambobin gungun da kudin jabu da darajar su ta kai Pounds 500,000 na Sudan, da ma sauran wasu kudaden kasashen waje.

Wata sanarwa da GIS ta fitar jiya Litinin, ta ce wannan ne karo na biyu cikin watan nan na Yuli, da hukumar ke nasarar damke gungun masu aikata wannan laifi.

Yayin sumamen da jami’an tsaron suka kai maboyar masu aikata wannan laifi, sun gano wasu manyan na’urorin kwafar takardu, da sauran sinadarai da suke amfani da su wajen gurza kudaden na jabu.

Tattalin arzikin kasar Sudan na fama da kalubalen raguwar darajar kudi, da kuma hauhawar farashin kayayyaki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here