Jam’iyyar APC a jihar Kano taron kasuwa ce – Mu’az Magaji

0
5145

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano da aka sallama daga aiki bisa zargin ya yi murnar mutuwar tsohon shugaban fadar gwamnatin Najeriya, Injiniya Mu’az Magaji ya ce jam’iyyar APC a jihar Kano ta zama taron Kasuwa.

Mu’az Magaji wanda ya wallafa haka a shafinsa na fasebuk ya kara da cewa akwai kuma jam’iyyar APC mai jama’a wacce gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ke jagoranta

“APC a kano ai taron kasuwace, Akwai APC cinye du …kowa ya santa da mambobinta tsirari..akwai kuma ta Maigirma Gwamna, APC Mai Jama’a ”

Wannan dai yana zuwa ne kwana ɗaya da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’anati wato EFCC ta gayyaci kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule domin ya amsa tambayoyi akan zargin mallakar wasu kadarori.

Tuntuni dai Mu’az Magaji ya dade da nuna sha’awarsa ta ne neman kujerar gwamnan jihar Kano a kakar zabe ta shekarar 2023, wanda ake ganin shi ma Murtala Sule Garo na da sha’awar kujerar ta gwamnan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here