Jam’iyyar APC ta afka cikin fushin ubangiji – Ayodele Fayose

0
452

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana rikicin da Jam’iyyar APC ta ke fama da shi a matsayin fushin ubangiji ne ya sauka akan jam’iyyar. La’akari da yadda jam’iyyar ta APC ta mayar da al’ummar ƙasar nan mataulata tare da ƙasa assasa maguɗin zaɓe da kuma yin riƙon sakainar kashi da al’ummar ƙasar nan a daidai lokacin da dubbai su ke rasa rayukansu.

Fayose ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a game da rikicin da jam’iyyar APC ta ke ciki.

“Jam’iyyar APC ta nuna ƙarfin mulki tare da yin amfani da ɓangaren shari’a wajen tsoratar da ƴan Najeriya”

Ya ƙara da cewa wannan somin taɓi ne da jam’iyyar ta APC ta fara ganin rikici, domin rikinci yana gaba kamar yadda kakakinsa Lere Olayinka ya bayyana.

A ƙarshe ya ce Najeriya ta sauka daga turbar ci gaba bayan da jam’iyyar APC ta karbi ragamar shugabancin ƙasar nan, ya ce jam’iyyar APC ba za ta taɓa rabuwa da rikici ba, har sai rikicin ya shafeta daga doron  ƙasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here