Jam’iyyar APC Ta Kama Da Wuta A Jihar Kano

1
4482

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Wutar rikicin siyasar cikin gida da ta kunno kai a tsakanin Shugaban jam’iyyar APC reshen Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas Ɗan Sarki da kuma tsohon kwamishinan ayyuka Eng. Mu’azu Magaji waɗanda manyan makusanta ne ga gwamnan Jihar ta Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda hakan ke nuni da cewar jam’iyyar APC ta kama da wuta a Jihar Kano duba da kusancin da kowane ɗaya daga cikinsu ya ke da shi da gwamna Ganduje.

Abdullahi Abbas dai shi ne shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma ya na da matuƙar tasiri da faɗa aji a gwamnatin Jihar Kano. Haka zalika shi ma Mu’azu Magaji duk da cewar gwamna Gandujen ya sauke shi daga kan kujerarsa ta kwamishinan ayyuka biyo bayan katoɓarar da ya yi akan marigayi Abba Kyari, amma daga baya ya ba shi a matsayin shugaban zartarwa na kwamitin aikin shimfida bututun iskar Gas daga Ajakuta zuwa Kaduna zuwa Kano, wanda hakan ya ke nuni da cewar duk da ya sauke shi a kan kujerar kwamishina amma har yanzu ya na da fada a wurinsa.

An dai ruwaito Mu’azu Magajin ya na shaguɓe da gugar zana ga shugaban jam’iyyar ta APC reshen Jihar Kano Abdullahi Abbas Ɗan Sarki har ma ya danganta shi da mutum mahaukaci wanda bai cancanta ya zama shugaban jam’iyya ba. Kamar yadda ya ɗora hotonsa ya ke cewa:

“Wannan shine Jagoran jamiyyar siyasa a Kano….Jaha kamar kano ace mai irin wannan toshahshiyar kwakwalkwar fahimtar mene ne ma dimokradiyya, ache shi ne jagoran mu a siyasa! Wato ma yan jamiyya, da jama’ar Kano…bama su da amfani a tinaninsa”. Wannan na ɗaya daga cikin kalmomin bayyana tsamin dangantaka da Mu’azu ya furta akan Abdullahi Abbas a shafinsa na Facebook.

Ba a nan kaɗai ya tsaya ba har sai da ya yi waiwayen baya ya kawo sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Gwale wacce ke zaman mazaɓar Shugaban jam’iyyar inda ya ke nuni da cewar ko mazaɓarsa bai iya kawo wa ba. Ga abin da Mu’azun ya ce:

“Ga sakammakon, karamar hukumar Gwale a zaben da ya gabata na, 2019.
PDP: 50,834
APC: 12,284”. Haka dai Mu’azu Magajin ya ke a shaguɓe da gugar zana har ma da sanya hoton shugaban jam’iyyar ya na caccakarsa a shafinsa na Facebook.

A wani yanayi da ke nuni da yadda shugaban jam’iyyar ya magantu akan kalaman na Mu’azu Magaji a wurin taron rantsar da shugabannin jam’iyyar ta APC da aka yi yau a gidan gwamnatin Kano ya roƙi gwamna ganduje da ya sanya hukumar tantance lafiyar ƙwaƙwalwa su auna masa lafiya ƙwaƙwalwar duk waɗanda ya ba wa muƙamai a matakan gwamnatinsa daban-daban.

A cewar ɗan Sarkin gwamna Gandujen ya na kitso da ƙwarƙwata saboda ya ga ana ba wa mutanen da su ke zare idanuwa su na tanɗar baki su na zagin shugaban ƙasa su na zagin gwamna su na zagin minista su na zagin shugaban jam’iyya inda ya bayyana hakan a matsayin aikin ƙwaya har ma ya nemi gwamna Gandujen ya tsince su daga cikin jam’iyyar su je su haɗu da ƴan ƙwaya ƴan uwansu.

Kalaman na Abdullahi Abbas su na nuni ne da Mu’azu Magaji kaitaye a matsayin martani akan irin maganganun da ya ke yi a kansa. Wannan dai shi ne lamarin rikici na baya-bayan nan da ke kunno a tsakanin mutanen da ake yi wa kallon ƴan gaban goshin gwamna Ganduje rikicin da ake hasashen zai iya zama wata barazana ga jam’iyyar ta APC a zaɓen a shekara ta 2023 ko ma ya sharewa jam’iyyar adawa ta PDP hanyar hawa kan madafun ikon Jihar.

Akwai irin wanna dambarwa a tsakanin tsohon gwamnan Jihar ta Kano Eng Rabi’u Kwankwaso da tsagin Gandujiyyar wanda ko da a yau ɗin sai da shugaban jam’iyyar ta APC Abdullahi Abbas ya nemi kwankwason ya ɗebo ƴaƴansa ya zuba a cikin siyasa kamar yadda su su ke yi in ya so a mutu har su tunda ya ce siyasar 2023 ko a mutu ko a yi rai. Sannan shi ma a nasa tsagin Ɗansarkin ya bayyana cewa a mutu ƙurmus ma.

Irin wannan rikici dai na manyan ƴan siyasa da jam’iyyu ba wani sabon abu ba ne a tarihin siyasar Jihar Kano da ma ƙasa ba, sai dai akwai buƙatar magoya baya su riƙa yin hattara ka da su riƙa zaƙewa duba da yadda irin wannan taƙadama a iya cewa mace ce mai ciki ba a san mai za ta haifar ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here