Jam’iyyar PDP ta yabawa Buhari akan yadda aka samar da tsaro a zaɓen Edo

0
1566

Gabanin zaɓen gwamnan jihar Edo da za a gudanar a ranar Asabar din nan mai zuwa, jam’iyyar PDP ta yabawa shugaba Muhammadu Buhari akan yadda ya sanar da wadataccen tsaro a faɗin jihar.

Sanarwar jinjinawa shugaba Buhari na cikin ƙunshin sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP reshen jihar ta Edo, Mista Nehikhare ya sanyawa hannu a madadin shugaban jam’iyyar na birnin Benin.

Mista Nehikhare ya ce ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi na samar da tsaro tare da baiwa al’ummar jihar Edo kariya abin a yaba ne.

Ya ƙara da cewa la’akari yadda gwamnatin tarayya ta kawo rundunonin jami’an tsaro zuwa jihar ta Edo, jam’iyyar PDP tana da ƙwarin gwiwar samun zaɓe wanda babu rikici a cikinsa. Ya ce hakan kuma zai ƙarfafi gwiwar masu kaɗa ƙuri’a wajen fitowa ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin kaɗa ƙuri’arsu ba tare da wata fargaba ba.

A ƙarshe sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su fito domin zaɓar shugabannin da su ka ca ncanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here