Jihar Katsina ba ta taɓa shiga mawuyacin hali irin wanda ta ke ciki ba – Ahmed Adamu

0
422

Wani malamin jami’ar Nile da ke Abuja kuma dan asalin jihar Katsina, Dakta Ahned Adamu ya bayyana cewa jihar Katsina ba ta taɓa samun kan ta a cikin mawuyacin hali kamar a wannan lokacin ba.

Dakta Ahmed Adamu ya bayyana haka ne a shafinsa na fasebuk.

“Jihar Katsina ba ta taɓa samun kan ta a cikin irin wannan mawuyacin halin na ƙuncin tattalin arziki da taɓarɓarewar tsaro kamar wannan lokacin ba. Tun bayan da hukumomi su ka ƙargame iyakokin ƙasar nan aka samu ƙaruwar mabarata akan titunan Katsina da kuma gidaje, rashin ya ta’azzara haka kuma uwa uba ga rashin aikin yi da ya ke ƙara ta’azzara”

Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke cigaba da kai hare hare ba tare da kaukautawa.

Mazauna jihar na dora alhakin wadannan hare-hare kan gazawar hukumomi.

A cikin watan nan ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron kasar nan umarnin kaddamar kakkabe ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a jihar ta Katsina, sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindigar.

A watan jiya, uban kasar Batsari da ke jihar ta Katsina ya shaida wa manema labarai cewa akwai kimanin mata 600 da aka bari da marayu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mazajensu.

Mazauna yankunan jihar Katsina na ci gaba da zama cikin yanayi na zullumi da fargaba sanadiyyar harin ‘yan bindiga da ke satar jama’a don karbar kudin fansa da ake yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here