Jirage 17 Makare Da Kayan Abinci Za Su Iso Legas

0
466

Hukumar lura da tasoshin ruwa ta Nijeriya, NPA ta bayyana cewa tana sa ran isowar jirage sha bakwai dauke da man fetur da kayayyakin abinci zuwa tashar ruwa ta Legas daga 19 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yuli.

NPA ta bayyana hakan ne a cikin takardar da ta buga mai taken `Shipping Position’ kuma ta raba a Legas a ranar Juma’a.

Bayanai daga takardar sun nuna cewa; jiragen na dauke da busasshen kifi, man gyada, kwantenoni na abinci, jirgin Cargo, Suga da dai sauran su.

Inda suka tabbatar da cewa an tanadi wadansu jiragen guda 19 domin kwasar wadannan kayayyakin abincin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here