Jonathan Ya Bi Sahun Atiku: Bai kamata a zubar da jini ba – Goodluck Jonathan

0
2150

Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce “bai kamata a kashe wani ɗan Najeriya ba” yayin zanga-zangar lumana da aka shafe kwanaki ana yi ta neman gyara ayyukan ‘yan sanda a ƙasar.

Jonathan ya ce duk da cewa akwai mabambantan ra’ayoyi tsakanin ‘yan Najeriya game da al’amuran ƙasa, amma akasari manufar guda ɗaya ce.

“Babu jinin ɗan Najeriya ko ɗaya da ya kamata a zubar yayin zanga-zangar lumana domin neman cigaban ƙasarmu,” in ji Jonathan cikin wani saƙon Twitter.

“Muna iya samun mabambantan ra’ayoyi game da lamuran ƙasa amma tabbas akasari manufar guda ɗaya ce ga Najeriya; ƙasar da za mu rayu cikin ni’mar da Allah Ya yi mana.

“Ina kira ga kowa da kowa da a zauna lafiya a irin wannan lokaci mai wuya.”

A jiya ne dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai kamata jami’an tsaron ƙasar nan su ɗauki matakin harbi ko bindigewa ba ga masa zanga-zangar ƙin jinin rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a ƙasar nan wato SARS ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here