Kadoji sun mamaye tituna a jihar Alabama dake Amurka

0
2754

Wasu manyan kadoji sun mamaye titunan wasu yankunan jihar Alabama a Amurka (USA) da mahaukaciyar guguwar Sally ta yiwa barna.

Fiye da gidaje 400,000 da wuraren kasuwanci sun kasance ba su da wutar lantarki saboda ruwan sama mai ƙarfi a Florida da Georgia, da Alabama.

Hanyoyi da gadoji sun zama marasa amfani saboda ambaliyar ruwa a yankin.

Guguwar ta haifar da ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashin jihohin Carolina da Virginia, da Alabama.

Kadojin sun mamaye tituna a Gulf Shores a Alabama sanadiyar ambaliyar ruwan da ta sanya su fitowa daga guraren da suke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here