Kano: Wata Kotu ta nemi a tono mamaci daga kabarinsa

0
269

Wata Kotun shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta bayar da umarnin tono wani mutum daga kabarinsa bayan mako daya da binne shi.

Mataimakan shugaban hukumar Hisbah ta jihar mai kula da ayyuka na musamman Sheikh Muhammad Al-bakri ne ya tabbatar wa BBC wannan lamari a ranar Talata.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Sani Yola ce ta bayar da umarnin a yi wa gawar sutura kasancewar hukumar Hisbah ta roki kotun da ta bai wa asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano umarnin bayar da gawar wani mai suna Abdullahi Obinwa ga iyalansa domin binnewa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Bayan wannan umarni ne kuma aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Igbo mai suna Basil Ejensi.

Hakan ya sa wasu ‘yan kabilar Igbo garzayawa kotun Ustaz Ibrahim Sarki Yola inda suka bayyana wa kotun cewa an yi musu musayar gawa.

Bayan ta saurari jawabinsu ne kuma, kotun ta bayar da umarnin a hako gawar da ta bayar da umarnin binnewa mako guda da ya gabata.

A cewar Al-bakri, janyewar da shaidu suka yi ne ya sa kotun ta yanke hukuncin bayar da gawar.

Sai dai kawo yanzu, ba a san inda gawar wancan mutumin da hukumar ta Hisbah take da’awar cewa ya musulunta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here