KARIN WUTAR LANTARKI: Majalisa Ta Dakatar

0
50099

A ranar Litinin ne, shugabannin majalisar wakilai da ta Dattijai a Nijeriya sun dakatar da batunn karin kudin wutar lantarki da ta ki ci ta ki cinyewa.

A kwanakin baya ne aka yi shirin fara amfani da sabon tsarin karin kudin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli na wannan shekara, amma majalisar ta yi nasarar gamsar da kamfanonin dake samar

Hakan na kumshe ne a wata sanarwa da mai baiwa shugaban majalisar Dattijai shawara na musamman kan kafafen watsa labarai Ola Awoniyi ya fitar.

Shugaban majalisar Dattijai, Ahmad Lawal, da kuma kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da sauran masu mukamai na majalisun guda biyu sun yi zama tare da mukarraban gwamnatin tarayya masu kula da sha’anin wutar lantarki a fadin kasar.

Zaman ya hada har da shugabannin kwamitin lantarki na majisar wakilai da Dattijai.

Shugabanin Majalisar sun nuna rashin dacewar kara kudin wuta a daidai wanan lokaci duk da akwai bukatar hakan. Su ma a nasu bangaren hukumar dake kula da sha’anin wutar sun nuna basu gama kammala shirin su ka karin kudin ba. Daga karshe an cimma matsaya a zaman, koda za a kara kudin sai a shekarar baɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here