Ko gobe a dawo zaɓe mu ABBA za mu yi a Kano – Ali Artwork

0
322

Fitaccen tauraron fina-finan Hausa, kuma Edita a masana’antar Kannywood, Aliyu Mohammad Idris, wanda akafi sani da Ali Artwork, ya bayyana cewa soyayyarsu da ɗan takarar gwamnan Kano a tutar Jamiyyar PDP Kwankwasiyya a zaɓen shekarar 2019, Injiniya Abba Kabiru Yusuf mutu – ka – raba.

Ali Artwork ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk, inda masu bibiyar sa a shafin su ka kafsa muhawara tare da bayyana ra’ayinsu akan wannan batun.

“Ko gobe a dawo zaɓe mu ABBA za mu yi a Kano” in ji Ali Artwork

Abban dai, Abban Kanawa, Abban Kwankwasiyya” 

Kalaman na Ali Artwork na zuwa ne a daidai lokacin da wata jita – jita ta game kafafen shafukan sadarwa na zamani akan Abba Gida-Gida ɗin na shirin raba tafiya da ɗariƙar Kwankwasiyya.

Sai dai ɓullar wannan labari ya sanya Abba Gida – Gida fitar da sanarwa ta hannun mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai Ibrahim Adam, inda ya ke ƙara jaddada goyon bayansa ga Madugun ɗariƙar Kwankwasiyya da ma duk wani abu da ya shafi harkokin siyasar PDP Kwankwasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here