Ganin cewa mafi yawan fyade da ake yi wa kananan ‘yan mata a Kano, yana faruwa ne a tsohon kangon ginin da ba a gama gina shi ba, gwamnatin Kano ta bada shelar cewa duk wani mai tsohon kangon gina a jihar ya gine shi ko kuma a daure shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ya bayyana haka ranar Alhamis.
Haruna ya ce a dalilin haka jami’an tsaro za su rika bin duk wani kagon gini dake jihar suna cafke wadanda ke boyewa ciki suna tafka barna.
” Duk wanda aka kama da laifin aikata wani mummunar abu a irin wani kangon gini, toh laifin zai shafi harda mai mallakin wannan gini.
Abdullahi Haruna ya yi kira masu irin wadannan gine-gine a jihar da su gaggauta gine su tun da w uri.