Ko kun san al’adar Sarakunan Kano idan su ka ziyarci hubbaren Shehu Mujaddadi?

0
4046

A yau mai martaba Sarkin Kano da mai martaba Sarkin Bichi su ka kai ziyara ga hubbaren Shehu Mujaddadi Shieyk Uthman Bin Fodio(Rahimahullah).

Maƙasudin sa wannan rubutu da hoto shi ne mutane su ga ya tsarin kai ziyara ya ke ga hubbaren Shehu Mujaddadi duk da cewa ba a bukatar magana mai tsaho ba ko kushe wani bangare sai dan gyara saka makon yadda wasu masana tarihi a lokacin wancan sarkin suka yi kuskure fahimta abinda ya faru a waccan ziyara ta wancan sarkin suna gani sai an cire rawani ko an dage amawali kamar yadda yayi wancan lokacin kafin a shiga hubbaren wanda ina kyautata zaton sun fadi haka ne bisa rashin fahimta ko buncike inda suke ce:

“Wai al’adar sarakunan Kano ce idan suka shiga hubbaren shehu su cire rawani dan nuna ladabi”

Wanda kuma ba haka bane hujja ita ce duk sarakuna suna shiga hubbare ne da rawanin su takalma ne kadai ake cirewa saboda ladabi shi ko rawani siffa ce ta cikar kamala kuma shiga ce ta Ma’aiki Alaihisalam wanda kuma inda cire rawani a gaban kabari alama ce ta nuna girmamawa to ashe saka shi zai iya zama kuskure ne kuma bazai zama siffa ce ta sarakuna kasar hausa ba?

Kuma da al’ada ce cire rawani inda ba a samu hoto ko wani rubutu na tarihi dake nuna wani cikin sarakunan Kano yayi haka kafin wannan lokaci wanda kuma basu da hujja bayyananiya da take nuna haka kafin wannan lokaci ko kuma wata hujja ta ilimi da hakan yake da tushe da addini tunda tsarin mulkin an kafa shi ne bisa addini da jihadi shehu Mujaddadi. 

 

Na biyu daga wannan hoton mutane zasu gane tunda ga shi wasu daga cikin sarakuna hakiman sokoto a cikin hubbaren Shehu amma ba mutum daya yayi abinda suke fada yana daga tsarin daular Sokoto duk sarkin dake karkashin tutar jihadi darajarsa tana dai dai ne da dukkan hakimi ga sarkin Musulmi.

 

Sanin kowa ne daular Sokoto an kafata bisa tsarin addinin musulunci karkashin Tariqa Qadiriyya ta Shehu Abdulkadir Jilani wanda yake jika ne ga sayyadina Hussaini jikan Ma’aiki Alaihisalam wanda kuma dukkan sarakuna Kano kafin zuwan Tijjaniya ita ce tariqa da suke bi har zuwa sarkin Kano Abbas wanda shi ya fara shiga Tariqa Tijjaniya.

 

Wanda shi wannan saka rawani da Sarakuna suke Shehu Mujaddadi(Rahimahullah) da kansa yayi magana a game da rawani a cikin Littafinsa IHYA’U SUNNA ya kawo sunnar yadda ma’aki yake sanya rawani da abubuwan da aka karhanta(wanda ba a so ) ga me da saka rawani da kuma abubuwan da mutane suka qirqiro na bidi’a wanda wasu ke da karancin fahimta game da hakan inda duk wanda ke bukatar sani game da haka ya neme wannan littafi dan yin cikakken bincike game da haka(Sunnar yin rawani). Wanda in kuma har wanda auke ganin cirewa dai dai ne suna da wata hujja ta hoto ko a wani sannen littafi na addini na magabata a shirye muke da mu karbi hujjarsa

 

A karshe bisa ladabi da girmamawa ba nayi rubutun nan bane dan qalubalantar abinda ya farun bane ko ina danganta shi da wancan Sarkin ko a matsayin kuskure busa kyakyawan tunani game da shi kansa wancan sarki kasancewar sa mutum ne mai bincike da kuma bibiyar abubuwa da karba shawara a wajen kowane ya bashi wanda kuma ta iya kasancewa hakan ta faru ne wancan lokacin bisa wata hujja ta kansa ko kuma mashawarata dake tare dashi wancan lokacin kasancewar shi mutum ne mai giramama ra’ayi da neman sani akan abinda duk bai sani ba. Wanda ko kwanan nan a karatu da yake wani ya yi masa yar matashiya amma nan take aka dauka kuma aka gyara.

 

Kassim Tijjani Turaki ya rubuto daga Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here