Sakamakon wani binciken da aka gudanar a baya-bayan ya nuna cewa, duk da cewa kasarsu ce a kan gaba wajen ci gaban tattalin arziki, Amurkawa sun fi kowa kunci a duk fadin duniya.
Sakamakon wannan binciken da kamfanin Gallup ta gudanar ta hanyar gwada ingancin rayuwar mutane dubu 151 wadanda suka fito da sama da kasashe 140,ya nuna cewa a shekarar da ta gabata kashi uku cikin hudu na wadanda ke fama da kuncin rayuwa Amurkawa ne.
An auna nagartar rayuwar mutanen a sikelin kyawawa da kuma munanan ababen da suka fuskanta a rayuwarsu.Abinda yasa aka gano cewa a wadannan ‘yan shekarun 10 Amurkawa sun fi kowa kunci,rashin wadatar zuci, tsoro da kuma fushi a duk fadin duniya.
A tsakiyar nahiyar Afirka kuma, Cadi ce ke a sahun gaba a jerin kasashen da suka fi fama da tashe-tashen hankula a bara.Kasashen yammacin nahiyar bakar fata Nijar da kuma Saliyo ne mara wa Cadin baya a matsayin a matsayin na uku da kuma hudu.
A yankin Latin Amurka, Paraguay ce kasar da ta fi kowacce ingantacciyar rayuwa da kuma kwanciyar hankali da lumana.
Paraguay na ci gaba da rike wannan mukamin tsawon shekaru da dama.