Ko kun san ƙasar da sai maza sun je ‘gidan mahaukata’ kafin su angwance?

0
3621

Alkaluman gwamnati na nuna cewa daga shekara ta 2009 zuwa watan Maris, mata 385 ne suka fuskanci cin zarafin da kan kai ga kisa a kasar Peru saboda banbancin jinsi.

A kusan kashi 70 cikin dari na wadannan lamura, ana dora alhakinsu ne kan ko dai abokan zaman matan ko kuma wadanda suka taba aurarsu a baya.

Matsalar dai ta yi kamari a kasar Peru ta yadda kananan hukumomi ke son bullo da shirin da zai bukaci gabatar da shaidar rashin tabin hankali kafin a yiwa ma’aurata rajistar aure.

Hukumar kula da matsa ta kasar ce ta gabatar da wannan tsari.

Tana bukatar a rinka gwada mazan da ke neman aure domin sanin cewa ko suna da tabin hankali ko kuma a’a.

Fatan da ake da shi, shi ne cewa wannan gwajin zai sa a rinka gano wadanda basu da hankali da rashin kwarewa da sauran halayen da ka iya lalata dangantakar aure.

“Ba wai kawai za ta taimaka wurin kaucewa asarar rayuka bane, za kuma ta karfafa aure a wani rukuni na rayuwa da ke bukatar cikakken hankali kafin a yi shi da kuma girmamawa a kasa kamar Peru inda ake fama da tashe-tashen hankula”, kamar yadda Mabel Magellan, ta kwalejin koyon fasahar nazarin tunanin dan adam da ke Lima, ta shaida wa BBC Mundo.

Sai dai Claris Ocana kwararriya kan lamuran da suka shafi tabin hankali na da banbancin ra’ayi: “Cin zarafin mata ba shi da alaka da hankali ko rashinsa, sai dai halittar maza ta bukatar mata”.

Gwaji ne kawai?

Sai dai hukumar kula da matasan na matsa kaimi kan shirin nata, tana mai cewa tana da goyon bayan Majalisun kanan hukumomin Peru (AMPE), don haka nan gaba kadan za a fara amfani da shi a kananan hukumomi.

Ko wannan zai hana mutanen da ke da tabin hankali samun damar yin aure?

Sai dai René Galarreta, ta hukumar kula da matasan ta ce takardar shaidar “ba za ta zamo sharadin yin aure ba.”

“A maimakon haka duk wanda yake da tabin hankali ko wani abu makamancin wannan, to za a duba lafiyarsa sannan daga bisani ya yi aure”.

A cewar Mabel Magellen, “manufar ita ce a san halin da lafiyar mutane ke ciki.”

“Idan mutum ba shi da hankali ko yana da matsala a kwakwalwarsa, to ma’auratan za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana. Akwai yiwuwar a gano abubuwan da kan kai ga tashin hankali da kuma shawo kansu,” a cewarta.

“Bai kawo karshen matsalar ba”

Sai dai kungiyar mata ta Demus na ganin wannan ba ita ce hanyar da ya kamata a shawo kan lamarin ba.

“Manufar bata shawo kan matsalarba. Samun bayani kan lafiyar hankalin ma’aurata ba zai kawar da cin zarafin mata ba.”

Masana halayyar dan adam na cewa lamarin na da alaka da ‘tabin hankali’, wanda ke kawar da hankali daga ikon da mutum ke da shi a tsari irin na gargajiya wanda ya bashi ikon saduwa da macen da kuma ci mata zarafi.

Rahoton BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here