KORONA: Kungiyar FAHIMTA Ta Raba Wa Mata Kayayyakin Abinci A Bauchi

0
59

Kungiyar ‘Fahimta Women and Youth Development Initiative (FAWOYDI),’ ta raba kayayyakin abinci da abin wanke hannu ga mata 250 a kananan hukumomi biyar a jihar Bauchi.

Shugabar kungiyar, , Hajiya Maryam Garba, ita ce ta bayyana hakan a yayin raba kayayyakin a Bagoro da kuma karamar hukumar Kirfi a ranar Lahadi a Kirfi.

Ta ci gaba da cewa; sun raba kayayyakin ne dominn rage radadin da al’umma suka fada sakamakon annobar cutar Korona, inda ta ce wadanda suka amfana da wannan tallafin sune wadanda suke fuskantar matsalar tattalin arziki.

Daga cikin abubuwan da aka raba sun hada da shinkafa, masara, Taliyar spaghetti ga mata 75 a Bagoro inda wasu 75 suka amfana a Kirfi wadanda yawancinsu marasa galihu ne. Kuma kungiyar ta ce ta raba kayayyakin wanke hannu da takunkumin fuska domin dakile yaduwar annobar korona.

Sauran kananan hukumomin da suka amfana da wannan tallafin sun hada da; Giade, Alkaleri da Bauchi. Inda mata 100 suka amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here