Korona: Malamai Sun Koma Makaranta A Oyo

1
125

A ranar Litinin din nan ne mafi yawan Malaman da suke karantawar a makarantun gwamnati sun koma baki aiki domin bin umurnin da gwamnatin jihar ta bayar na cewa a koma makaranta.

Rahotanni sun bayyana cewa da misalin karfe 8 na safiyar Litinin, Malaman da aka ga sun bayyana musamman a makarantun da suke garin Ibadan, suna da yawan gaske. A yayin da wasu makarantun Malaman da suka zo ba su wuce uku zuwa hudu ba kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.

Kwamitin da ke lura da dakile annobar cutar Korona a jihar Oyo, a karkashin gwamnan jihar, Seyi Makinde ya bada umurnin dalibai da suke aji 6 a firamare, da wadanda suke aji 3 a karamar Sakandare da wadanda suke aji 3 a babbar Sakandare da su koma makaranta a ranar 6 ga watan Yuli, a yayin da kuma ya umurci Malamai su koma a yau Litinin 29 ga watan Yuni. Inda kuma suka bi umurninsa a yau.

Wadansu shugabannin makarantar sun shaidawa majiyarmu cewa Malaman sun samu horo na musamman kan yadda za a dakile yaduwar cutar ta Korona, kuma tuni suka suka  horas da sauran wadanda ba Malamai ba, domin ganin an dakile yaduwar cutar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here