Korona Ta Dakatar Da Hukumar Tsaro Ta NSCDC Daukar Sabbin Ma’aikata

0
74

Hukumar tsaron NSCDC ta Nijeriya ta dakatar da daukar sabbin ma’aikatan da za ta yi sakamakon annobar cutar Korona dake yaduwa a kasarnan.

Sanarwar dakatar na dauke ne da sa hannun jami’in hulda da kafafen watsa labarai na Kwamandan hukumar, Ekunola Gbenga.

Hukumar ta ce za ta sake sanar da ranar da za a tantance wadanda suka nemi aiki da hukumar, inda ta tabbatar da cewa wadanda suka aika da neman aiki da hukumar tuni aka tattara sunayen wadanda aka hukumar ta tantance za ta gayyace su.

Bayanai sun nuna cewa an bai wa hukumar tsaron ta NSCDC damar daukar ma’aikata dubu goma wadanda za su taimaka wajen yaki da matsalar tsaro a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here