Ku ci gaba da wanke hannu idan ba haka ba cutar korona na nan dawowa – Ministan Lafiya

0
191

Ministan Lafiya na ƙasa Osagie Ehanire, yayi gargadin cewa la’akari da yadda ƴan Najeriya ba sa bin dokokin dakile yaduwar cutar korona, cutar kan iya dawowa nan ba da jimawa ba.

Osagie Ehanire ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Legas.

Ministan yayi kira ga kafafen yada labarai da su rika yada ka’idojin da ya kamata abi wajan kaucewa kamuwa da cutar ta korona.

Ya ƙara da cewa ƙa’idojin su ne wanke hannu, Nesa-nesa da juna da kuma saka takunkumin rufe baki da hanci.

Idan za a iya tunawa dai a daren ranar juma’a ne hukumomi suka sanar da harbuwar mutum 170 a kwana ɗaya, abin da ya kawo adadin wadanda cutar ta harba zuwa dubu 62 da dari 6 da 91, mako na 13 a jere da adadin wadanda wannan cuta ta kama ke zuwa kasa da dari 3.

Sai dai an samu mutane 3 da cutar ta kashe, lamarin da ya kai adadin mamata zuwa dubu 1 da dari da 44, kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka ta kasar ya nuna.

A cikin makonni 2 da suka wuce, adadin wadanda cutar ta aika barzahun sun kasance a kasa da 10.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here