Ku kawar da ta’addanci maimakon kama masu zanga-zanga – Auwal Rafsanjani

0
213

Ƙungiyar rajin tabbatar da ayyukan majalisa masu alfanu a ƙasar nan wato CISLAC, ta yi tir da kama ɗaya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya da ‘yan sanda su ka yi.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun daraktanta, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani.

CISLAC ta ce ta kadu sosai duba da yadda ta ga an yi watsi da mutuntu ‘yancin demokradiyya da na ‘yan kasa.

An kama Nastura Ashir Shariff da safiyar jiya Laraba 17 ga watan Yuni, bayan da ya halarci wata zanga-zanga wacce kungiyarsu ta CNG ta shirya domin alhinin kashe-kashen da ake yi a jihar Katsina.

A cewar CISLAC, “amfani da karfin jami’an tsaro kan masu zanga-zangar lumana zai iya haifar da tashin hankali maras tushe.”

An kama Nastura ne bisa zargin cewa ya zagi mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina.

Tuni matasa da dama suka nuna fara bayyana bacin ransu kan shafukan sada zumunta domin kama Nastura da aka yi.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Najeriya ita ma ta fitar da wata sanarwa kan shafin Twitter inda ta umarci hukumomin kasar nan da su sake shi cikin gaggawa.

A cewar Amnesty “Nastura bai yi wani laifi ba, kawai ya fito ne domin fafutukar kawo karshen rashin tsaro a arewacin kasar nan”.

Ita dai CISLAC ta jaddada yadda “hukumomi ya kamata su yi amfani da karfin da suke da shi wajen kawo karshen ta’addanci wanda ya mamaye yawancin sassan kasar nan, maimakon kama masu zanga-zangar Lumana.”

A cewar dokokin kasar nan, mutane suna da ‘yancin yin zanga-zanga da fadin albarkacin bakinsu da kuma ‘yancin a mutunta su.

Bisa wadannan dokokin ne CISLAC ta yi kira da a saki Nastura da duk wadanda aka kama ba bisa doka ba cikin gaggawa.

Duk hakan na faruwa ne bayan karuwar kashe-kashen mutane da ake yi a yankunan arewacin kasar nan, musamman ma a jihar Katsina.

Lamarin da ya tunzura CNG shirya zanga-zang a domin nuna bacon ranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here