Kwankwaso ya Bayyana hanyoyin da shugabannin za su bi don hana sata a Najeriya

0
3244

Wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriya ya yi iƙirarin cewa za a ci gaba da sace dukiyar raya yankin Neja Delta da ma sauran ma’aikatun ƙasar, matuƙar shugabanci ba zai zura ido kan kuɗaɗen da ake fitarwa ba.

Matuƙar ba za a yi ƙoƙarin tabbatar da ganin kowanne kobo an yi amfani da shi a inda ya dace ba, ba shakka za a ci gaba da samun matsaloli wajen tsare amanar dukiyar al’umma, in ji Rabi’u Musa Kwankwaso.

Tsohon gwamnan Kano wanda ya taɓa aiki a matsayin wakili cikin kwamitin gudanarwar hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) kafin ya yi murabus a 2010, na wannan jawabi ne ta cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa.

Jigon ɗan adawar ya nuna cewa mayar da hukumar ƙarƙashin ofishin shugaban ƙasa, ba lallai ne ya yi wani tasiri ba, don kuwa a baya ma an taɓa yin hakan ba tare da samun sauyin a-zo-a-gani ba.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Majalisar Najeriya ta ce a mayar da kuɗin hukumar NDDC da aka kwashe cikin wata uku ba bisa ƙa’ida ba, sakamakon binciken badaƙalar kuɗi N40bn.

Binciken dai ya yi matuƙar tayar da ƙura a ƙasar tare da fito da gagarumar matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu kuma take addabar Najeriya.

Kwankwaso ya faɗa a cikin shirin cewa ya yi murabus daga hukumar ne saboda abubuwan da suke faruwa a lokacin sun saɓa da tunani da aƙidarsa ta inganta rayuwar al’umma.

“Ran da zan bar aiki, mun zo mun zauna…. Muna zaune aka zo ana magana da shi manajan darakta a kan waɗansu biliyoyi(n kuɗi) da ake zarginsa da cewa ya ɓatar da su.

Ina zaune sai na ga yana dariya. Ni na ɗauka ma yana da amsa. Amma a ƙarshe….. Sai na ji ashe ma gaba ɗaya, shi gani yake wannan ba matsala ba ce,” in ji shi.

A cewarsa: “Kuma su ma ragowar mafi yawan waɗanda muke aiki da su, suna tuhumarsa ne saboda suna ganin (manajan daraktan) ya yi musu dungu”.

An tambaye shi ko wanne yunƙuri ya yi musamman lokacin da yake ɗan majalisar dattijai don ganin an kawo sauyi kan yadda ake gudanar da harkoki a hukumar raya yankin Neja Delta, Kwankwaso ya ce matsalolin ne suna da yawa a ƙasar.

 

‘Rashin kulawar shugabanni na taka rawa’

Ya ce muhimmin abu dai shi ne shugaban da al’umma ta zaɓa, shi ne ya fi kowa sanin matsaloli na kowanne sashe da kuma yawan kuɗaɗen da ake warewa sassan hukumomin gwamnati.

Sanata Kwankwaso ya ce jazaman sai shugabanci ya zage dantse, kuma dole sai an ɗauki mataki tare da hukunta jami’an gwamnatin da aka samu da aikata ba daidai ba.

Ya ɗora alhakin mummunan cin hancin da ake zargin tafkawa a hukumar NDDC kan halayyar zalama ta son tara abin duniya da kuma rashin kulawar shugabanci a ƙasar.

“Sau da yawa, mutane za su aikata wasu abubuwan da zai janyo gurguta tattalin arziƙi na wani sashe ko na ƙasa gaba ɗaya, kuma shi ke nan kuma sai a ci gaba da tafiya a haka.”

A cewarsa matsalar satar dukiyar al’umma ba ta taƙaita a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya ba. “In dai babu cikakken tsari na shugabanci, na tabbata kuɗaɗe ga su nan ko’ina. Har a jihohi,” in ji shi.

Ya ce duk waɗannan abubuwa da ake ganin suna faruwa, inda shugabanni suna kula sosai da irin maƙudan kuɗaɗen da ake fitarwa har ta kai ga an ciyo basuka, kuma a ɓarnatar da su, da ba a yi su ba.

 

‘Kuɗaɗen da ake warewa Neja Delta sun ƙazanta’

Shi ma, Dakta Janaidu Muhammad wanda ya taɓa aiki a matsayin kwamishina cikin hukumar raya yankin Neja Delta tun lokacin da aka kafa ta da sunan OMPADEC, ya ce duk da maƙudan kuɗin da ake fitarwa don raya yankin, “amma sai ka je ka taras ba komai”.

Ya yi iƙirarin cewa jagororin da ake damƙa wa alhakin raya yankin Neja Delta kan ɓarnatar da dukiyar da aka warewa yanki, su ma fitar da kuɗin ƙetare inda suke gina tamfatsa-tamfatsan gidaje.

“Kuma ko me aka yi musu, (suna ganin) ba daidai aka yi ba, in dai ba bari aka yi, aka yi facaka da dukiyar ba,” in ji Dakta Janaidu. “Ko zuwa ka yi za ka wuce…. gani suke yi tamkar ka je ka ɗebi kuɗinsu ne”.

Tsohon ɗan siyasar na jamhuriya ta biyu ya kuma soki lamirin manufar keɓe wa yankin ƙarin kuɗi na musamman har kashi 13% a matsayin albarkar ma’adanin da ake haƙowa a yankin.

Ya ce yawan kuɗaɗen da ake warewa don raya yankin na Neja Delta “sun ƙazanta, duk da yake kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba”.

Dakta Janaidu ya shawarci rushe ko dai hukumar raya yankin Neja Delta ko kuma ma’aikatar raya yankin don kuwa a cewarsa duk aiki ɗaya suke yi.

A cewarsa mummunan kuskure ne kafa ma’aikatar raya yankin Neja Delta duk da yake, akwai hukuma guda da aka kafa tun tuni don yin aiki da ma’aikatar za ta yi.

Rahoton BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here