Lafiya Uwar Jiki: Shan taba sigari alama ce ta taɓin hankali – Binciken Masana

1
2250

Wasu likitoci dake jami’ar ‘St. Louis’ sun bayyana cewa masu fama da tabuwar hankali sun fi masu cikakken hankali yawan shan taban sigari.

Likitocin sun gano haka ne a wani bincike da su ka gudanar kan wasu dake fama da tabuwar hankali da ake kula da su. A nan ne suka ga cewa lallai masu dan matsala a kwakwalwar su su ka fi shan taba fiye da wadanda su ke kalau.

Jagorar binciken Farfesa Li-Shiun Chen ta ce mafi yawan masu shan taba suna son su bari amma hakan ya gagara. Sannan kuma idan har ma sun warke daga cutar ma rabuwa da tabar ya kan gagara.

A ƙarshe Li-Shiun Chen ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya na asibitocin mahaukata da su taimaka musu wajen ganin sun kubuta daga wannan dabi’a wato shan taba sigari.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here