Laifin satar kaji ya sanya shugaban ƴan sanda ya kashe wasu matasa da taɓarya a caji ofis a Bauchi

0
3478

Lamarin ya faru ne bayan ɗan sandan ya yi wa wasu matasa uku duka da taɓarya a caji ofis.

Ɗaya daga cikinsu ya tsira da karaya iri-iri. Ana zargin matasan ne da sace kaji na wani mutum a birnin Bauchi.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan Adam kamar Human Rights da Amnesty International da ma wasu kungiyoyi na cikin gida sun sha zargin jami’an tsaron Najeriya da keta hakkin bil Adama ciki har da kisa ba tare da shari’a ba da azabtarwa da sauransu.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce ta kafa kwamiti domin binciken azabtarwar da kuma kisan matasan da ake zargin ɗan sandan ya yi.

Abdulwahab Bello, shi ne matashi daya tilo da ya tsira da ransa daga azabtarwar da ake zargin jami’i ɗan sandan ya yi masu. Abokansa biyu sun mutu sanadiyyar duka da taɓarya da ake zargin wani babban jami’in dan sanda ya yi masu a caji ofis.

Abdulwahab ya ce shi magini ne, amma da abokansa biyu suka zo da kaji guda bakwai, ya raka su kasuwa suka sayar da su, amma daga bisani sai aka ce ana zargin kajin na sata ne.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here