Lalacewar shugabancin Bala Muhammad a jihar Bauchi ne ya sa na fice daga PDP – Dogara

0
4077

Tsohon shugaban Majalisar Wakilan ƙasar nan Yakubu Dogara ya bayyana dalilan da suka sa shi ya sake sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC bayan shugaban riko na Jam’iyyar Mai Mala Buni ya sanar da komawar sa cikin Jam’iyyar ta su.

A wasikar da ya rubutawa Jam’iyyar PDP a mazabar sa ta Bogoro, Dogara yace rugujewar shugabanci a Jihar sa ta Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed da ya taimakawa samun nasara shi ne dalilin da ya sa ya bar Jam’iyyar.

Dogara yace ba zai iya bude baki yayi tambaya kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Jihar ba sai a zarge shi da rashin biyayya, saboda haka ya haure takalman say a fice daga Jam’iyyar.

Tsohon shugaban Majalisar yace idan ya naɗe hannayen sa yaki cewa komai kan yadda al’amura ke tabarbarewa a Jihar Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed zai zama maci amana, bayan a lokacin Gwamna Isa Yuguda da Mohammed Abubakar kowa ya ji muryar sa ya na bayyana ra’ayin sa idan yaga ba daidai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here