Lokaci Ya Yi Na Kawo Karshen Matsalar Shan Wiwi -Majalisar Dinkin Duniya

0
177

Ofishin yaki da shan miyagun kwayoyi da aikata muggan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya UNODC, ya nemi matakan shawo kan matsalar durkushewar tattalin arzikin duniya don gudun jefa manoma cikin halin tasku.

Wasu sabbin bayanai da Ofishin yaki da shan miyagun kwayoyi da aikata muggan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya UNODC ya fitar, sun ce masu safarar miyagun kwayoyi na cin karensu ba babbaka a lokacin wannan annobar Korona, akasarin ma’aikata a kasashe kamar Afganistan da wasu na yankin Latin Amurka sun tsinci kai a aikin gonaki da ake noma tabar Wiwi don samun kudade.

DW Hausa a rahotonta ta ce; rahoton ya gargadi gwamnatoci da su dauki matakan shawo kan matsalar durkushewar tattalin arzikin duniya don gudun jefa manoma cikin halin da ba su da zabi fiye su tsunduma noma harmatattun ganye irinsu tabar wiwi. Baya ga haka ma dai an gano alkaluman yawan masu ta’amalli da miyagun kwayoyin ya karu sosai tun bayan bullar annobar da ta sanya takaita zirga-zirga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here