Ma’anar Ɗan Jarida Da Abubuwan Da Su Ka Zama Wajibi Ga Duk Wani Ɗan Jarida Ya Kiyaye A Cikin Aikinsa 

1
322

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Yau Ce Ranar Ƴan Jarida Ta Duniya, Albarkacin Wannan Rana, Na Fito Muku Da Muhimman Abubuwa Da Su Ka Shafi Ɗan Jarida Da Aikinsa, Sannan Kuma Ina Amfani Da Wannan Dama Na Jinjinawa Ƴan Uwa Jajirtattun Ƴan Jarida Tare Da Addu’a Ga Waɗanda Su Ka Mutu Allah Ya Ji Ƙansu Ya Gafarta Musu.

-Aikin Jarida Aiki Ne Mai Matuƙar Kima Da Daraja, Sannan Kuma Aiki Ne Da Ya Ke Buƙatar Taka-Tsan-Tsan Matuƙa, Bayan Ɓangaren Zartarwa Da Ɓangaren Majalissa Da Sashen Shari’a, Ƴan Jarida Su Ke Riƙe Da Dimokaraɗiyya A Duniya.

Yau Lahadi, 3 Ga Watan May, 2020.
Mafi yawan mutane masu sha’awar zama marubuta su na da sha’awar aikin jarida. Su na kuma da burin su fita su samo labarai ko neman shuhura da kambun girmamawa da ɗaukaka da lambobin yabo waɗanda duka su na faruwa da ƴan Jarida. Sai dai kuma abu ne da ke buƙatar ɗaukar dogon lokaci wajen samun ƙwarewa kafin a tura ka dukkar wani aiki da ka ke da sha’awa.

Ɗan jarida mutum ne da ya ke samo labari. Lokaci shi ne ɗan jarida. In ma mutum ya na rubutu ne ya fito lokaci-lokaci ko kuma ya na rubutu ne a gidan jarida, akwai buƙatar ka tabbatar da cewa rubutunka ya na da lokaci. Akwai buƙatar ka tabbatar da cewar maƙasudin labaranka sun shafi al’umma ne kaitsaye. Wannan shi ne ginshiƙin aikin kasancewarka ɗan Jarida.

Idan ka na tunanin zama ɗan jarida ya zama wajibi ka kiyaye da waɗannan dokoki:

(1). Yin Daidaito Ga Kowane Ɓangare: Idan abu ya faru a ɓangarori guda biyu, wajibi ne a aikin jarida ka ji ta bakin kowane ɓangare ka kuma yi wa kowa adalci. Duk ɗan jarida wanda ya san abin da ya ke zai saurari kowane ɓangare ne ya kuma buga labarin na bangaren da su ke ƙorafi da waɗanda ake ƙofarin a kansu.

(2). Kiyayewa Da Lokaci: Lokaci abu ne mai matuƙar muhimmanci a aikin Jarida. Ya zama wajibi ɗan jarida ya kiyaye da lokaci a labaransa. Ba daidai ba ne ga ɗan jarida ya ɗauko labarin da ya faru shekaru 20 da su ka wuce ya ce zai buga shi a yanzu, face sai idan wannan labari ya na da alaƙa ne da labarin da ya faru a wannan lokaci. Akwai buƙatar ɗan jarida ya maida hankali wajen samo labaran da su ke faruwa a halin da ake ciki.

(3). Tabbatar Da Gaskiyar Labari: wajibi ne ɗan jarida ya kasance mai bin diddigi da nazari da bincike mai zurfi kafin ya buga labari, ya tabbatar da cewar duk abin da zai faɗa haka ya ke babu daɗi babu ragi.

Idan har ka samu ilimi kan waɗannan dokoki guda uku ka kuma yi aiki da su, to aikinka na jarida zai tafi cikin nasara. Ko da ka karya doka, to ka da ka damu. Sai dai kawai ka kiyaye ka da ka sake maimaita karya dokar agaba. Wasu daga cikin al’umma su na son koyon abu ne ta hanyar gwadawa, ina ɗaya daga cikinsu, sai dai idan ka karya jigon aikin jarida to aikin ba zai gamsar ba.

A matsayin ɗan jarida, aikinka ya tanadar da bibiyar labaran al’umma. Kuma ka tabbar da gaskiyar al’amari da kuma lokacin da ya faru. Ya zama wajibi ka rubuta gaskiya kan duk abin da ka ji da abin da ka gani ka kuma ba wa al’umma damar bayyana ra’ayinsu. Sannan kuma ka bayyana haƙiƙanin majiyar da ka samo labaranka a duk lokacin da za ka wallafa labarai a matsayin aikin jarida.

Sannan kuma a matsayin ɗan jarida ka kiyaye da sautinka ka gano shi idan ya faɗo cikin rubutunka. Ka da ka yi mamaki idan edita ya sake wallafa rubutunka a karon farko. Wani abu da za ka ƙara kiyayewa a lokacin da ka fara aiki a matsayin ɗan jarida, ka da ka ƙyamaci aikin, a kullum ka riƙa sanyawa zuciyarka ƙaunar aikin. Ka da ka damu idan edita ya ƙi karɓar wani sakin layi na rubutunka ko kuma ya yi maka wasu gyare-gyare a ciki, domin aikinsu su ke yi. Cikin ƙanƙanin lokaci za ka fahimci editan su kuma gane tsarin rubutunka.

A mafi yawan lokuta ɗan jarida ya kan samu aiki a matsayin mai ɗauko rahoto, kuma ɗauko rahoto da shi kansa gundarin aikin jarida ayyuka ne da su ke sauyawa. Amma mafi yawan al’umma su na tunanin aikin jarida rubutu ne a manyan gidajen jaridu na duniya, Ilimin shi ne zai ba ka damar kasancewa mai ɗauko rahoto a wata jarida ko kuma ka zama marubuci a wata mujalla, duk abu ne guda ɗaya, kowa aikin jarida ya ke yi. Muddin ka na aikin jarida, to ka shirya tsintar kanka a kowane irin sashe na aikin jarida kai dai kawai ka kiyaye da manyan sharuɗan aikin jarida kan duk abin da za ka rubuta.

Mafi yawan al’umma su na jin cewa masu aikin nemo labarai iya labarai kawai su ke aikewa tare da yabawa ƴan jaridar da su ka yi aikin binciken labarin sosai, sai dai lamarin ba haka ya ke ba, domin kuwa mafi yawan masu aikewa jarida labarai su na tabbatar da adalci ga kowan ɓangare a ya yin gudanar da bincike kan labaransu. Waɗanda su ke aikewa da labarai akan laifuffuka a wani sashe da kotuna a wasu lokutan editoci ne waɗanda su ke tabbatar da adalci da kuma bincike mai zurfi kan labaransu. Dan haka akwai buƙatar mutum ya yi gaggawar koyon wannan idan ya na aikin jarida, yawan kallonka ga labari gwargwadon yadda zai zo maka da inganci. A wasu lokutan ka na da lokacin da za ka yi hakan, sauran lokutan kuma sai ka yi aiki akan lokaci.

Ya zama wajibi in ka na aikin jarida ka maida hankali wajen ba wa lokaci muhimmanci. Ba ma wannan kaɗai ba hatta a wajen rubuta labarai ya zama wajibi ka kiyaye da lokaci, wannan babban horo ne ga duk wani marubuci, iya yawan rubutunka iya yawan yadda za ka tabbatar da ya fita cikin inganci akan lokaci. Dan haka aikin jarida aiki ne da ya ke da matuƙar kima da daraja a duk duniya. Sannan kuma ba kara zube ake shigarsa ba, aiki ne wanda ya ke buƙatar kafin ma ka shige shi ya kasance ka na da sha’awar yinsa sannan kuma ka na da juriya da jajircewa da kiyaye dokokinsa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here