Mafi Yawan Barayin Nijeriya Sun Boye A Ghana –Shugaban EFCC Magu

0
183

Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC na riko, ya bayyana cewa mafi yawan barayin Nijeriya suna boye ne a kasar Ghana.

Magu ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a Abuja, inda ya ce hukumar na tatttara bayanai wuri guda domin dawo wa da kudaden Nijeriya da aka sace aka jibge a kasar ta Ghana.

Shugaban EFCC din ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar CIPRMP suka kai masa ziyara a hedikwatar hukumar.

A cewarsa, EFCC din tana hada hannu da takwararta na Ghana kan kudaden Nijeriya dake kasar domin tsara yadda za a dawo da su.

Magu ya ce rashawa ba shi da Katanga, inda ya ce suna kammala tattara bayanai za su shiga Ghana ba tare da wata sanya musu iyaka ba wajen kwato kudaden Nijeriya domin dawo da su gida Nijeriya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here