Mai ɗakin gwamnan jihar Kaduna ta gudanar taron gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar fyaɗe

0
7217

A wannan rana uwar gidan gwamnan Jihar Kaduna Hajiya Aisha (Ummi) Garba El-Rufa’i ta kammala wani taro na gaggawa da ta kira da manufar tattauna yadda za a samar da tsare-tsare tun daga tushe domin a kawo ƙarshen matsalar fyaɗe da cin zarafin jinsi da ke cigaba da zama wutar daji a Jihar Kaduna.

Taron wanda ya haɗa dukkan masu ruwa da tsaki na Jihar Kaduna waɗanda su ka haɗa da: Shugabannin ƙananan hukumomi da matansu da masu riƙe da sarautun gargajiya da shugabannin addinai da mata masu faɗa aji da matasa masu faɗa aji da shugabannin rundunar jami’an tsaron fararen hula Heads of Civil Defense, da shugabannin ƴan bijilanti Heads Vigilante Services (KADVS) da ƴan sa kai na cikin al’umma da sauransu.

A cikin jawabin da ta gabatar a wurin taron, uwar gidan gwamnan, Hajiya Aisha (Ummi) Garba El-Rufa’i ta yi kira ga duk waɗannan masu ruwa da tsaki da su gaggauta ba da duk wani haɗin kai da goyon bayansu domin a kawo ƙarshen matsalar fyaɗe da cin zarafin jinsi. Sannan kuma ta yi kira ga iyaye da su cigaba da sanya ido sosai akan rayuwar ƴaƴansu domin sanin waɗanda su ke mu’amala da su.

Daga nan uwar gidan gwamnan ta ƙara da yin kira ga iyaye da su kauda ɗabi’ar nan ta ɓoye laifin fyaɗe ga yarinyar da aka aikatawa domin hakan ne zai ba da damar nemowa yarinya haƙƙinta a gaban shari’a.

Daɗi da ƙari, ta kuma buƙaci iyaye da su riƙa koyar da ƴaƴansu yadda za su riƙa kwarmata ihu a duk lokacin da wani ya nemi lalata da su domin a kai musu agaji. Daga nan kuma uwar gidan gwamnan ta ƙara da yin kira ga al’umma da su zama masu sanya ido haɗi da fallasa asirin duk wanda ya aikata laifin fyade.

Daga bisani kuma uwar gidan gwamnan ta nuna jadawalin tsarin yadda za a samar da hanyar sadarwa mai ƙarfi wacce za ta haɗa duk masu ruwa da tsaki tun daga kan shugabannin ƙananan hukumomi da matansu har zuwa kan masu sanya ido kan matsalar fyaɗe da cin zarafin jinsi. Ta bayyana cewa wannan tsari zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen matsalar fyaɗe a Jihar Kaduna. Sannan kuma tsarin zai shafi duk ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin Jihar.

Sauran waɗanda su ka gabatar da jawabi a wurin taron sun haɗa da shugabannin addinai inda su ka gabatar da bayanai kan hukuncin fyaɗe a mahangar addinana.

A cigaba da tsare-tsaren da ta gabatar a wurin taron ta yi bayani ga jami’an tsaro na ƴan sanda akan abin da ya kamata a fara yi cikin gaggawa a duk lokacin da aka samu hatsarin afkuwar fyaɗe ta yadda za a je cibiyoyin lafiya matakin farko idan aka samu rauni ko zubar jini ga wacce aka yi wa fyaɗen kafin a kai ga Sexual Assault Referral Center (SARC).

Daga nan kuma sai uwar gidan gwamnan ta ƙara yin kira ga iyaye musamman mata da su riƙa binciken cikin sassan jikin ƴaƴansu domin gano ko akwai wata matsala da ke nuni da an ci musu zarafi.

Da ta juya kan malaman addinai kuwa, uwar gidan gwamnan ta yi kira ga malaman addinai da su riƙa gabatar da waɗannan batutuwa na fyaɗe da ke faruwa a cikin huɗubobinsu na mako-mako domin ganin an samu nasarar kawo ƙarshen matsalar gabaɗaya.

Uwar gidan gwamnan ta kuma yi kira ga matan shugabannin ƙananan hukumomi da su haɗu da ita su ƙara tattaunawa duba da rawar da za su taka tun daga tushe domin kawo ƙarshen wannnan matsala. Sannan ta ƙara da yin kira ga duk masu ruwa da tsaki daga kowacce ƙaramar hukuma da su yi aiki tare da tsare tsaren da aka yi tun daga ƙaramar hukuma har zuwa mazaɓu domin samun haɗin kan da zai ba da damar yaƙar matsalar.

Daga cikin manyan baƙin da su ka halarci taron sun haɗa da:

Kwamishinan ilimi Malam Shehu Maƙarfi da na ƙananan hukumoni Alhaji Jafaru Sani da Shaikh Jamilu Albani daraktan hukumar, Bureau of Interfaith da Shaikh Muhammad Kabiru Gombe da Rev. Joseph Hyab na ƙungiyar CAN ta Kaduna da Malam Rabiu Abdullahi na Fitiyanul Islam.

Sai kuma Bishop Yusuf Janfalan da Rev Daniel Kasuwa da Alkali Murtala Nasir Al-Misiri da Pastor Aderan United Pastors da Rev Kasuwa da Dr. Yusuf Ibrahim Kubau da Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu Sheikh Makari Sa’eed da Malam Ibrahim Kufena sec. JNI da Dr. Bello Abdulkadir Salanken Zazzau da sauran sun haɗa da Munir Jaafaru Yariman Zazzau da Bunun Zazzau da Tukuran Zazzau da Hasheem Bindawa da Alhaji Tahir Mahmoud.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here