Mai Mala Buni Ya Zama Shugaban Rikon Majalisar Zartasawa Na APC

0
87

Majalisar Zartaswar Jam’iyyar APC ta nada gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko bayan rusa Majalisar Gudanarwa da aka yi yau Alhamis a yayin wani taron da ya gudana a fadar shugaban kasa.

Mai taimaka shugaban kasa kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad shi ne ya wallafa haka a shafinsa na Twitter. Wanda ya ce an yi hakan ne domin barakar da ta kunno kai a cikinta wadda take kokarin raba kan shugabanninta.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar da gwamnonin jihohi da ake zargin suna goyan bayan jigon Jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu ba su halarci taron ba.

RFi Hausa sun labarto cewa; wadanda aka tabbatar sun halarci taron sun hada da gwamnonin Jihohin Nasarawa da Neja da Jigawa da Filato da Imo da Kogi da Yobe da kuma Osun.

Sauran sun hada da na Jihohin Ogun da Legas da Kwara da Kebbi da Kano da Kaduna da kuma Ekiti.

Jam’iyyar APC ta fada rikicin shugabanci tun bayan da kotun daukaka kara ta tababtar da dakatarwar da aka yi wa shugabanta Adams Oshiomhole, inda mutane da dama suka fito suna ikirarin cewa, sune halartattun shugabannin Jam’iyyar.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana goyan bayansa ga jagorancin Victor Giadom a matsayin shugaban riko, matakin da ake ganin ya saba wa matsayin Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa wadanda ke goyawa Hilliard Eta baya, bayan an amince ya rike wa Sanata Abiola Ajimobi kujerar sakamakon rahsin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here