Mataimaki Na Musamman Ga Shugaban NECO Ya Ajiye Mukaminsa

0
76

Kasa da makonni biyu da nada shi a matsayin mataimaki na musamman ga Magatakardar hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta NECO, Dr Emeka Flemin Okengwu, ya ajiye mukaminsa.

Ajiye mukamin da Dr Emeka Flemin Okengwu, ya biyo bayan tursasawa da Magatakardar Farfesa Godswill Obioma yake fuskanta akan ya sauke shi a mukamin, a daidai lokacin da wata kungiya da ta kira kanta APC-AG, wacce ta yi zargin cewa Dr Emeka ba memba bane na jam’iyyar APC, a don haka ba za su yarda ya rike wannan mukamin da ya kamata a ce wadanda suka yiwa APC wahala ne aka bai wa ba.

Farfesa Godswill Obioma bayan matsin da ya sha, majiyarmu ta shaida mana cewa, sai Magatakardar ya shawarci Dr Emeka akan ya ajiye mukaminsa ba tare da bata lokaci ba a maimaikon ya zama an kore shi ne.

Majiyarmu ta ce bisa wannan shawarar ne Dr Emaka ya ajiye mukaminsa, wanda ya ce hakan zai ba shi damar maida hankali a sauran ayyukan da suke kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here