Mataimakin Gwamnan Ondo Ya Gudu A APC Ya Koma PDP

0
88

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi ya fice daga jam’iyyar APC inda ya arce zuwa jam’iyyar PDP.

Ajayi  ya fice daga APC din ne a mazabarsa dake Ward 2 a Apoi, dake karamar hukumar Ese Odo a jihar.

Sai dai rahotanni sun ce ya zuwa ranar Litinin ake sa ran zai koma PDP a hukumance a Sakatariyarsu dake Akure.

Bayanai na nuni da cewa alakar dake tsakanin mataimakin gwamnan Ajayi da gwamna Oluwarotimi Akeredolu ta yi tsami a cikin watannin nan. Barinsa APC ya kawo karshen rade-radin ficewarsa a jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here