Matsalar Tsaro: Ƴan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Zamfara

0
1352

An sace shugaban ƙaramar Hukumar Bakura da ke mazabar Gamji ta jihar Zamfara wato Sani Dangwaggo na Jam’iyyar APC.

Majiyar iyalansa ta ce, da misalin karfe 11 na daren da ya gabata wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da shi daga gidansa da ke unguwar Gamji a daidai lokacin da ake shatata ruwan sama.

Sakataren Yada labaran Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Shehu Isa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a ƙasar nan, matsalar da har yanzu hukumomin kasar suka gaza magance ta.

 

Rfi Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here