Mayaƙan Boko Haram 602 sun yi mubaya’a ga gwamnatin Najeriya

0
3387

Hedikwatar Tsaro ta ce tubabbun ‘yan Boko Haram 602 sun yi rantsuwar mubaya’a ga gwamnatin Najeriya.

Darektan yada labarai na Hedikwatar Tsaro Manjo Janar John Enenche ya ce tsoffin mayakan na Boko Haram din sun kammala horon da aka ba su na tuba, tare da yin watsi da munanan akidun da za su hana al’umma karbar su idan suka koma gida.

Ya ce rantsar da su wata dama ce a garesu na kara tabbatar da biyayyarsu da mika yuwa da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Najeriya.

Enenche ya kuma ce tubabbun za su iya rasa duk wata dama da aka ba su idan aka same su da aikata laifin da ya saba wa dokar kasa.

Ya ce shirin na Operation Safe Corridor ya yi nasarar raba tubabbabun mayaka 882 da mummunar akidarsu kuma daga cikinsu an riga aka yaye mutum 280.

“Wannan sako ne ga wadanda ke cikin daji su zo su mika wuya domin cin ribar irin wannan yafiyar”.

Enenche ya kuma yaba irin kokarin da soji ke yi, musamman a wannan lokacin na ragargazar ‘yan ta’adda da lalata musu makamai a Jihar Borno da kuma farmakin sojin sama da ke kaiwa na tarwatsa ‘yan bindiga a Zamfara.

Ya ce a dan tsakanin nan, sojoji sun kwato mutum biyar da aka yi garkuwa da su a garuruwan Isa da karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Ya kuma ce, Sojojin Operation Sahel Sanity da taimako sojin sama sun yi kashe ‘yan bidiga shida a wata arangama da suka yi a tsaunin Komani na Jihar Zamfara inda aka kwato bindigogi da babura 34.

Ya ce, a cikin makonnan sun kwato dabbobi 714 da aka sata, wadanda suka hada da shanu 302 da tumaki 41 2 a jihar Zamfara.

Kabiru Matazu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here