Mayakan Boko Haram Sun Hallaka Ma’aikatan Agaji A Jihar Borno

0
184

Boko Haram sun yanka ma’aikatan agajin da suka sace a arewa maso gabashin Nijeriya a watan da ya gabata.

Kungiyoyin agaji na Action against Hunger da International Rescue Committee sun tabbatar cewa ma’aikatansu na cikin wadanda aka kashe.

Boko Haram sun sace ma’aikatan agajin ne a jihar Borno a watan Yunin 2020. A wani faifan bidiyo da aka fitar a watan jiya din an nuna yadda ma’aikatan agajin da aka kama suke yin bayani.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dora alhakin kisan kan kungiyar Boko Haram, tare da shan alwashin hukunta makasan. Inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da an ga bayan kungiyar Boko Haram.

Haka zalika, shima gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna kaduwarsa bisa wannan aika-aikar na kashe ma’aikatan agajin.

Kungiyar Action Against Hunger ta ce ta yi matukar kaduwa da kisan da aka yi wa ma’aikatanta duk da roko da magiyar da ta yi tana neman a sake su.

Ita ma kungiyar The International Rescue Committee ta ce ta yi matukar bakin cikin samun labarin kashe mata ma’aikata.

Mayakan boko Haram sun sha far wa ma’aikatan agaji kuma sau da dama suna kashe su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here