Muhammad Sanusi III ya bayyana a masarautar Kano

2
16902

Shafin Mai Kanon Dabo da ke dandalin Facebook ya wallafa hotunan Sanusi Aminu Ado Bayero cikin shiga irin ta sarauta.

Sanusi Aminu Ado Bayero wanda ya kasance ɗa ne ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kuma jikan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, ya bayyana sanye da rawani kunne biyu rike da sanda irin wacce Sarakunan daular Fulani ke riƙewa

Hotunan da aka wallafa sun yi kama da taya Sanusi Aminu Ado Bayero murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

“Allah ya ƙaro shekaru masu albarka Sunusi Aminu Ado Bayero”

“Dan Sarki Jikan Sarki, Muhammad  Sanusi  III”

Zuri’ar gidan Dabo dai na sanyawa ƴaƴansu Muhammad Sanusi da nufin mayar da Sarkin Kano Muhammad Sanusi I, wanda ya taɓa yin sarautar Kano.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here