Mulkin Buhari annoba ne ga ƴan Arewa – Solomon Dalung

2
7224

Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana jimamin sa kan kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya da Arewa Maso Yamma.

Dalung, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya bayyana bakin cikin shi game da yadda ake kashe ‘yan kasa a yankin Arewa duk da tsananin kashe kudin tsaro.

Dalung yace an kashe yawancin yan Najeriya mazauna Arewa a karkashin kulawar Buhari fiye da kowane lokaci a cikin tarihi.

Da yake magana da yaren Hausa, Dalung, wanda ya kasance minista a karkashin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana tsarin mulkin a matsayin wanda ya gaza.

Ya soki Shugaban kasar da laifin kyale jami’an tsaro su kwashe dukiyar al’umma ba tare da sakamako mai gamsarwa ba.

Ya ce, “Ya Shugaba, ka ba wadannan mutane karin kudi, duk da haka muna ci gaba da asarar rayuka da dama.

Wadannan mutane suna wadatar da kansu ne kawai da kudaden jama’a.

Abin bakin ciki, wani lokaci daya wuce ka ambata cewa sun ki bin umarninka; Ina nufin umarnin Kwamandan-In-Chief, don haka me ya sa har yanzu kake hakuri da su?

Shugaban kasa, lokaci yayyi da ka kyale su, saboda ci gaba da kasancewa a cikin su yana lalata tsarinka ne kawai.

Ni ba annabi bane amma zan iya yin hasashen cewa idan ba a dauki wani mataki akan wadannan masu cin amana a cikin gwamnatin ka ba, zaka yi nadama sosai a shekarar 2021.

Daga Borno zuwa Kwara, daga Filato zuwa Sokoto, rayuwar dan Adam ta zama mai sauki fiye da na kaza.

Misali, yadda rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba ke halaka, a kowane lokacin, kuma a garinka na jihar Kats ina.” a cewar Dalung.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here