29.2 C
Nigeria
Monday, September 27, 2021

Mun dakatar da kai kayan gwari kudancin Najeriya – Ƴan kasuwa

Must read

Masu sana’ar kayan gwari a jihar Kano sun bayyana cewa sun daina kai kayansu zuwa kudancin kasar nan biyo bayan lalata musu kaya da aka yi a baya bayan nan.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito shugaban kugiyar kasuwar gwari ta ‘Yankaba Alhaji Umar Ibrahim ya ce sun dauki matakin dakatarwar ne domin jan kunne.

Ya ce wasu batagari dake kudancin kasar nan ne suka tare musu kayayyaki suka kona na Konawa suka lalata wasu ya yin zanga-zangar #EndSA RS.

 

“Daga yanzu za mu dakatar da kai kayayykinmu zuwa kudancin kasar nan saboda barnan da aka yi mana.

Ya kara da cewa a yanzu haka muna dari-darin zuwa kudun saboda tsoron kada a afka mana a hanya.

“A farkon satin da aka fara yin zanga-zangar #EndSARS masu zanga-zangar suka kone motarmu cike da albasa a garin Fatakwal.

“Haka zalika bayan na Fatakwaldin, haka abin yaci gaba da mai-maituwa a garuruwan kudancin kasar nan.

“Adon haka ba zamu ci gaba da jefa kanmu cikin tashin hankali ba da sunan neman kudi” a cewar sa.

Kano Focus

- Advertisement -spot_img

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest article