Mutane 14 sun rasu sakamakon nutsewar jirgin ruwa a jihar Benue

0
1599

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa, a kalla mutane 14 sun rasu, yayin da wasu kuma suka bace, sakamakon nutsewar wani jirgin ruwa a ranar 5 ga wata, a jihar Benue dake yankin tsakiyar kasar nan.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, wannan jirgin ruwa mai dauke da mutane 23, ya nutse ne yayin da yake kan hanyarsa zuwa birnin Makurdi, babban birnin jihar ta Benue a wannan rana. Ya zuwa yanzu, an ceto mutane 2, yayin da kuma aka gano gawawwaki mutane 14, kana ba a san inda sauran mutanen suke ba.

Rundunar ‘yan sanda ta ce, dukkanin mutane dake cikin jirgin mambobin wata coci ne, sun kuma nufi birnin Makurdi domin halartar wani taro.

Ko da a ranar 3 ga wata ma, sai da wani jirgin ruwa mai dauke da mutane 21 ya nutse a birnin Lagos dake kudancin kasar, wanda ya haddasa rasuwar mutan e 7.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here