Na yi amfani da wani ɓangare na kuɗin auren ƴa ta na aurar da marayu 13 – Kabiru Marafa

0
391

Wani tsohon dan majalisar dattawa daga jihar Zamfara ya bayar da tallafin kayan daki ga wasu amare marayu su goma sha uku a garin Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

Yanzu haka dai marayun da suka amfana da wannan tallafi baki har kunne saboda tagomashin kayan dakin da suka samu kyauta kasancewarsu marayu da har ma suka fitar da ran samun kayan dakin.

Tsohon dan majalisar dattawan, Sanata Kabiru Marafa, ya ce ya bayar da wannan tallafi ne bisa la’akari da yadda ake da yawan marayu a cikin jihar wadanda ‘yan bindiga suka kashewa iyaye.

Tsohon sanatan ya ce: “A cikin jihar Zamfara a yanzu haka ba za a rasa marayu sama da dubu sittin zuwa dari ba, kuma wadannan marayu suna nan babu mai taimaka musu sai wanda ya dubi Allah ya ga ya dace ya yi wani abu.”

Ya kara da cewa: “Da aka tashi auren ‘yata, na yi mata nasiha a kan kada ta bari a yi mata almubazzaranci a bikinta akwai mabukata da za ta iya taimakawa da kudin da za ta yi wata hidima a bikin nata, kuma Alhamdulillah ta soke wasu bidi’o’i na bikin nata inda ta yi amfani da kudin nan har na taimaka wa wasu marayu goma sha uku da kayan daki.”

Ya ce, akwai marayu da dama da aka sanyawa ranar aure, amma kuma saboda babu ya sanya ana ta daga bikin, wannan ne “ya sa na ga ya dace na zakulo wadanda aka jima da sanya ranar aurensu domin na musu kayan daki ko a samu a kaw ar da su.”

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here