Najeriya ta samu shiga kwamitin tattalin arziki na Majalisar Dinkin Duniya

0
279

Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya ya amince da zaben Najeriya da wasu sauran kasashe 17 a matsayin mambobi a Kwamitin Tattalin Arziki na majalisar ranar Laraba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wa’adin sababbin mambobin kasashen zai fara ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021 kuma zai kasance na tsawon shekaru uku.

Wannan dai shi ne karo na uku da Najeriya za ta kasance mamba a wannan muhimmin kwamitin tun shekara ta 2012.

Kwamitin, wanda ke zama ruhin majalisar shi ne yake da alhakin juya akalar harkokin tattalin arziki, walwalar jama’a da kuma batutuwan da suka shafi muhalli na Majalisar.

A yayin zaben na ranar Laraba dai gurabe 14 ne aka ware wa kasashen Afirka, ragowar kujeru biyar ne kacal kuma aka fafata a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here