Najeriya ta yi adabo da cutar shan inna

0
153

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana wanke ƙasar nan daga cikin jerin kasashen dake fama da cutar polio bayan kwashe shekaru ana yaki da cutar.

Ofishin Hukumar dake Congo Brazzaville ya sanar da wanke kasar nan saboda rawar da hukumomin lafiya da kungiyoyin agaji da jami’an kula da lafiya suka taka wajen ayyukan rigakafi da wayar da kan jama’a wajen karbar maganin.

Hukumar Lafiya ta bayyana wannan rana a matsayin mai dimbin tarihi wajen kula da lafiyar jama’a a Najeriya da Afirka da kuma duniya ta fannin yaki da cutar polio wadda ta nakasa yara da dama.

Gwamnatin tarayyar kasar nan dai ta bayyana wannan nasara a matsayin gagarumar cigaba ga al’ummar kasar wanda ya nuna jajircewa wajen harkar kula da lafiyar al’umma.

Dr Faisal Shuaibu, Babban Daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko ya bayyana wannan lokaci a matsayin mai dimbin tarihi ga gwamnati da jami’an kula da lafiyar da suka taka rawa wajen samun wannan nasara.

Dr Shuaibu yace bayan gwamnatin Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jami’an kula da lafiyar da suka taimaka wajen samun wannan nasara, ba za’a manta da mutane irin su Aliko Dangote da Bill Gates ba saboda yadda suka sadaukar da dukiyoyin su wajen ganin an yaki wa nnan cuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here